A cewar rahoton da Kamfanin Dillancin Labaran Hauza ya tattara, yayin da aka shiga rana ta biyar da gudanar da zaman makokin goman farko na watan Muharram na shekara ta 1448 Bayan Hijira (Yuni, 2026M), garuruwa daban-daban a Nijeriya, da suka hada da Dass (a Jihar Bauchi), Sakkwato, Saminaka (a Jihar Kaduna), da kuma Maiduguri, sun shaida gudanar da tarukan tunawa da shahadar Imam Husaini (AS) cikin tsari, natsuwa da kuma halartar dimbin al'umma.
Wadannan tarurruka, wadanda 'yan'uwa Musulmi almajiran Sheikh Ibraheem Yaqoub Zakzaky (H) suka shirya a manyan masallatan juma'a, husainiyoyi da cibiyoyin addini na kasar, sun mayar da hankali ne ga bayyana darussan Ashura, karfafa hadin kai da kuma yin hidima ga al'umma. Wannan ya nuna kyawawan hotuna na soyayya da mika wuya ga iyalan gidan Manzon Allah (AS) daga mazauna yankin na Afirka.
1. Bayyana Koyarwar Ashura; Daga Sadaukarwar Sayyid Abbas (AS) Zuwa Kadaicin Jakadan Karbala
A bangaren jawabi da bayyana ma'anonin Ashura, malamai da masu wa'azi a garuruwa daban-daban na Nijeriya sun yi bayani kan muhimman darussan da ke tattare da yunkurin Imam Husaini (AS):
A Garin Dass: Malam Is'haka Zubairu Yalwan Dass ya gabatar da jawabi a harabar Babban Masallacin Juma’a na garin, inda ya mayar da hankali kan jigon hadin kai da dankon zumunci a tsakanin Musulmi, tare da bayyana jajircewa da sadaukarwar sahabban Imam Husaini (AS) a matsayin madubin koyi ga al'ummar yau.
A Garrin Sakkwato: Hussainiyatul Imamil Mahadi (ATF) da ke unguwar Mabera ta karbi bakuncin Alhaji Mustafa Umar Baba (Gadon Kaya). A cikin jawabin nasa, ya yi fashin baki kan matsayi na musamman na Abul Fadl Abbas (AS) a filin Karbala, inda ya bayyana jarumtaka da amincinsa wajen kare iyalansu a matsayin babban darasi na tsayawa kan gaskiya.
A Garrin Saminaka: Sheikh Umar Uba ne ya gabatar da jawabi a Hussainiyyar Shaheed Mahmoud Turi, inda ya bayyana tarihin rayuwa da shahadar Muslim bin Aqeel (AS), jakadan Imam Hussain (AS) zuwa Kufa, tare da jaddada muhimmancin cika alkawari da tsayin daka a tafarkin gaskiya.
2. Yunkurin Matasa Kan Tafarkin "Hidimta Wa Al'umma"
Daya daga cikin mafi kyawun abubuwan da suka faru a tarukan na bana shi ne yunkurin kishin kasa da hidima ga al'umma da matasa suka nuna a garin Maiduguri. Matasan yankin sun kaddamar da wani shiri mai suna "Hidimatun Nas" (Hidimta wa mutane), inda suka rika wanke takalma da yanke wa mahalarta taron da masu wucewa farce kyauta. Wannan aiki na jajircewa ya sami karbuwa sosai a wurin al'ummar gari, kuma ya nuna kyawun halaye na kaskantar da kai da hidima da aka koya a makarantar Karbala.
3. Fasahar Yara Da Matasa Wajen Hidimta Wa Tarihin Musulunci
Wani abin sha'awa da ya faru a lokacin taron shi ne gabatar da wasan kwaikwayo na tarihi da yara da matasa suka yi a garin Maiduguri. Wadannan yara sun yi amfani da fasaharsu wajen kwaikwayon yadda mutanen Kufa suka rika rubutawa da aikawa Imam Husaini (AS) wasiku suna neman ya jagorance su. Wannan salon fasaha ya taka rawar gani kwarai wajen isar da sakon Ashura da kuma sabar wa tsara ta gaba da tarihin Musulunci.
A cewar rahoton na Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, wadannan tarurruka masu albarka wadanda aka gudanar tare da wakokin makoki da addu'o'i, sun kammala cikin cikakken tsaro, natsuwa da lumana. Jajircewar mabiya Ahlul Bait (AS) a Nijeriya a wadannan kwanaki ya nuna cewa sakon Imam Husaini (AS) ya tsallake iyakokin kasa, kuma har yanzu yana matsayin madubin haske na yada zaman lafiya, sadaukarwa, adalci, da kuma taimakon bil'adama a duk fadin duniya.












Ra'ayinka